Anfara Rijistar Private NECO 2020/2021
ANFARA RIJISTAR JARRABAWAR PRIVATE NECO 2020/2021
A yau talata, 1st December, 2020 hukumar Jarrabawar Neco (National Examination Council) ta sanar da fara rijistar private Neco a shafinta na Twiter, a inda za’a kamala rijistar a ranar 22nd January, 2021.
- Yadda Za’ayi Rijistar/ abubuwan da ake bukata:
Duk dalibin da keda sha’awar yin rijistar private Neco ta shekarar 2020, wato (Senior School Certificate, External ) zai iya farawa da kansa ta www.neco.gov.ng ko kuma ya ziyarci interner café mafi kusa don yin rijistar akan lokaci.
- Dalibi zai iya sayan Registration Token da kansa ta hanyar zaiyartar website hukumar neco (www.neco.gov.ng) ko kuma yaje café mafi kusa don sayan Registration Token
- Hotan (passport size photograph ) da ake bukata shine mai farin baya (white background)
- Akwai dangwalen yatsu (biometric finger print) ga kowane dalibi a lokcin da akeyin rijistar.
- Dalibi ya sani cewar akwai tantancewa dangwalen yatsu ga duk dalibi kafin shiga dakin jarrabawa.
- Duk dalibin da aka kamshi yatsunsa basuyi dai dai ba a yayin tantancewa, hukumar zata tsare shi ta hukunshi kamar yadda doka ta tanadar.
- Tanan wannan website din ne kadai zaka iya yin rijistar www.neco.gov.ng
- Kudin sayan Registration Token shine N 9,850 sai N 50 dadi ta Stamp Duty
- Yadda za’a biya (mode of payment) dalibi zai iya saya da kansa ko ya biya a internet café a www.neco.gov.ng a inda zai biya nec bayan ya kirkiri account da email dinsa ko lambar wayarsa. Dalibi zai biya ta wadannan hanyoyi guda biyar (5)
- ATM card
- Internet banking
- USSD
- Wallet
- Bank branch
Dalibai su sani cewar a yanzu hukumar Neco bata printing kati(Scratch card) sedai Registration Token
- Lokacin faraway shine 1st December, 2020 za’a rufe 22nd January, 2021 da karfe 12:00 na dare
- Za’a karawa duk dalibin da baiyi rijista har 23rd January, 2021 zai biya tara ta N1000
- Hukumar na kara sanar da dalibai cewar zatayi tsarin nan na work in (sabon tsarin da hukumar NECO suka samar don gyaran wasu daga cikin subjects dad alibi ya rasa a jarrabarsa ta baya) akan kudi N 20,000 ga duk dalibi. Anayin wannan rijistar ne kafin ranar da za’a rubuta wannan jarrabar da kake bukata.
- A lokacin da aka gama yima dalibi rijista, za’ayi masa printing na wadannan abubuwa kamar haka:
- Timetable
- Photo card
Dalibin da ke da wata nakasa zaiyi rijista kamar yadda kowa yakey amma zaiyi nuni da irin nau’in nakasar tasa a lokacin yin rijistar.
Santar Yin Jarrabawa (examination centers) dalibi zai zaibi santar da tifi masa wadda ke cikin jerin santocin da hukamr Neco ta tabbatar a jahar sa.
Subjects da za’a iya dauka don yin jarrabawar suna kamar haka:
- Agricultural science
- Arabic language
- Biology
- Chemistry
- Civic education
- Christian religious studies
- Commerce
- Economics
- English language
- Financial Accounting
- French
- Further mathematics
- Geography
- Government
- Hausa
- Health education
- History
- Igbo
- Islamic studies
- Literature in English
- Mathematics
- Marketing
- Physics education
- Physics
- Salesmanship
- Stenography
- Store keeping
- Technical drawing
- Yoruba
Karin bayani (general information)
- Da zarar ka biya kudin jarrabawa to fa baza’a dawo maka das hi ba.
- Hukamar Neco na shawartar dalibi da ya nemi kwarerren interner café domin gujema afkawa kuskure. Hukumar bazata lamunci duk wani kuskure da aka fuskanta a yayin rijista. Sai dai kawai dalibi na dama guda daya (offline) da zai iyayin gyara kafin ayi submitting(online)
- Dalibi ko internet café da ya tabbatar ya duba website da hukumar ta tanadar domin yin rijista kafin ya fara rigista don kaucewa matsala.
- Wajibine dalibi ya karanta doka da oda da kuma jadawalin jarrabawar kafin faraway.
- Dalibi ya sani duk hotan da yayi amfani dashi a yayin registration to dashi za’ayi amfani a certificate.
- Dalibi ya tabbatar ya duba inda senta (center) da zaiyi jarrabawa alal akalla kwana daya kafin a fara jarraba.
- Shan taba, amfani da wayar hannu ko wani nau’in kayan sadarwa dokane yin amfani dasu a dakin jarrabawa.
- Dalibi zaisa kayansa na gida sannan ba’a yarda da zuwa da duk wani nau’I na makami ba.
- Ba’a yarda da yin rijista sau biyu ba, yin haka zai janyo soke duka biyun.
- Baza a lamunci shigar dalibi dakin jarrabawa bayan an fara.
- Wajibine dalibi ya sanya takunkumi (face mask) a dakin jarrabawa.
- Wajibine kowane dalibi ya taho da sanadarin wanke hannaye (hand sanitizer )
- Duk dalibin da yazo da wasu alamu na COVID 19 a yayin jarrabawa baza a barshi ya cigaba da zana jarrabawa ba har sai an tabbatar da ingancin lafiyarsa.
Good
Tnx
Muna godiya da wannan Labarai na gaskia. Allah ya Kaara daukaka
Muna Godiya