Education

Sakamakon Jarrabawar NECO Na Dab Da Fitowa

Sakamakon Jarrabawar NECO (National Examination Council)  dai na wannan shekara yana daga cikin sakamakon da daruruwan Dalibai ke jira saboda samun gurbi karatu a makarantar gaba da sakandare.

Iyayen dalibai da su kansu daliban sun koka bisa yadda sakamakon yayi duli wanda hakan yasa suke ta sunturi wajen masu café domin tuntubar su ko sakamakon ya fito domin su dora karatunsu daga inda aka tsaya.

Hukumar Jarrabawar da ta NECO tayi wata sanarwar sakin sakamakon a ranar 5 ga watan Oktoba 2021 za’a saki sakamakon wanda hakan bai samu ba har izuwa yanzu. Muna fatan wannan sakamako zai fito nan bada jimawa ba duba da irin lokacin daya dauka.

Arewatalent  ta tuntubi Hukumar NECO ta inda hukamar ta tabbatar da cewa da zarar komai ya kammala za’a sanar da sakin sakamakon ta kafar sada zumunta na wannan zamani, na hukumar nan bada jimawa ba.

Arewatalent ta tattauna da wani dalibi mai jiran jarrabawar ta NECO inda yace:

“Sakamakon Jarrabawar kawai nake jira saboda dashi zanyi applying na aikin Soja”

 Hakana wani dalibin ma yabayyanawa arewatalent cewa “NECO kawai yake jira domin samu gurbi a Jami’a”

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button