Education

Za’a Koma Makarantun Primary Da Secondary A Jihar Kano

Hukumar ilimi ta jahar kano ta sanar da ranar 18th January 2021 wadda za’a koma makarantun primary da secondary a fadin jahar. Wannan ta fito daga kwamishinan ilimi na jahar kana Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana cewar a ranar 18 ga januray dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu (private school) zasu koma kan karatunsu a matsalin lokacin da gwamnati ta rattaba hannu.

Hakana daliban dake makaratun kwana (Boarding Schools) zasu koma makarantunsu a ranar Lahadi 17th January 2021.

Kwanishinan ya roki iyaye dasu ja hankalin “yayansu wajan ganin sun koma makaranta akan lokacin da aka ajiye sannan ya kira hukumomin makarantu da kuma daliban don ganin sunbi dukkan sharuda ka’idoji domin kaucewa cuta me sarkewa nunfashi (COVID-19).

Sannan kuma kwaminishan ya nuna farin cikinsa da irin goyan bayan da iyayen dalibai ke bayarwa a duk lokacin da gwamnati ta sanya wata doka ko makamancin haka.

Sanarwa daga:                                                           

CPRO Ministry of Education Kano State

Aliyu Yusuf       

9th January 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button