Education

An Daga Da Kuma Bayyana Ranar Zama Jarrabawar Science And Technical Schools Ta Senior Secondary (SS)

Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga makarantun Science and Technical Schools, wato Science and Technical Schools Board, ta dage ranar fara jarrabawar Senior Secondary (SS) daga ranar Asabar 10th June 2023 izuwa ranar Lahadi 25th june 2023 na shiga wadannan makarantu.

Sai dai wannan dagewa bata shafi jarrabawar junior ba wato JS. Ita wannan jarrabawa ta JS tanan a wannan rana ta Asabar 17th June 2023. Dangane da haka ake bukatar dalibai da su zo wajan jarrabawar da kayan rubutu, cikakkun kayan makaranta da Slip na shedar rijista wanda aka cire a daga yanar gizo na wannan hukuma wato www.stsbkano.ng

Wannan sanarwa ta fito daga director mai kula da bibiyar makarantu da jarrabawa na gamayyar makarantun kimiyya da fasaha Malam Sunusi Aminu.

Jerin makarantun kimiya da fasaha dake a karkashin hukumar Science and Technical Schools Board, kano sune kamar haka :

  • Dawakin Tofa Science Collage
  • GTC Ungogo
  • Dawakin kudu Science Collage
  • GTC DawakinTofa
  • GTC Ungogo II
  • GSC Garko
  • GTC Sani Abacha
  • GTC Dambatta
  • GTC Gani
  • First Ladies
  • GTC Makoda
  • GTC Wudil
  • GTC Gaya
  • GTC Fagge
  • GTC Bagwai
  • GTC Rogo
  • Day Science Collage
  • GTC Karaye
  • GTC Gwarzo
  • Day Science Collage
  • GTC Karaye
  • Maitama Sule Gaya
  • GTC Dadin Kowa
  • GTC Bichi
  • GTC Gezawa
  • GTC Dawakin Kudu
  • GTC Kabo
  • Mairi Tijjani GSTC
  • GTC Kachako
  • GTC Nassarawa
  • GTC Tiga
  • Governor’s College Kano
  • GTC Bagauda
  • GTC Kano
  • GTC Albasu
  • GTC Gwale
  • GTC Minjibir
  • GTC Danbatta 2
  • GTC Kunchi
  • GTC Gabasawa
  • GTCTFA
  • GSTC Sumaila
  • New GSTC
  • GTC Warawa
  • GTC Rano
  • Phaug Jaoji
  • GSTC Dala

Domin cike daya daga cikin wadannan makarantu bayan an sayi scratch card sai a ziyarci kwararren Internet café mafi kusa domin yin registration.

Domin samun cikakken Karin bayani gameda wannan hukuma dama wadannan makarantu sai a ziyarci wannan shafi na hukumar Science and Technical Schools Board https://www.stsbkano.ng/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button