Education

Da Gaske Ne JAMB Ta Fitar Lokacin Sake Zana Jarrabawar 2022?

Yanar Gizo-gizo ta cika da bayanin cewa Jamb ta fidda sabon jadawalin zana jarrabawar na 2022 wanda dukkan dalibai masu sha’awar shiga Jamia da kwaleji ke jira domin dorawa inda aka tsaya da karatu.

Saidai lamarin ba haka yake ba hukumar ta Jamb bata fitar da jadawalin ba na 2022, munyi wannan bincike ne a cikin portal na Jamb domin tabbatar da sahihancin maganar saidai bamuga wannan Magana ba ta fara sayen form din.

Domin kuwa ga bayanai dake bayyana a portal din na jam cikin harshen turanci (JAMB HAS NOT COMMENCED THE SALE OF 2022 UTME/DE APPLICATION DOCUMENTS.)

Saidai Alamu sun nuna cewa hukumar dab take da sanar da ranar da Dalibai zasu fara yin rijista da kuma fara jarrabawar ta shekarar 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button