Education

JAMB: ePIN PAYMENT PROCESS BY CANDIDATES 2022

Hukumar JAMB ta fitar dukkan jadawalin yadda dalibai zasu sayi UTME ePin tareda bayyana  yadda kowane dalibi zaibi wajan sayan wannan pin kamar haka:

1.        Wajibi ne kowane dalibi yazamo yanada NIN kamar yadda hukumar JAMB ta tabbatar

2.        Za’ayi amfani da lamabar wayar da akayi rijistar NIN wajan tura sakon profile code.

3.        Za’a rubuta NIN sai a bada space sannan a rubuta harufa 11 na NIN (11 digits number) izuwa kodai 55019 ko 66019 misali: NIN 00123456789. (A tabbatar an bada “yar tazara a tsakani kamar NIN da lambobin). Za’a daura N50 charge na wannan service.

Note: A tabbatar sunan da aka turo ta hanyar profile code shi aka tura wajan sayan UTME ePin!

4.        Bayan anturo maka da profile code sai a garzaya izuwa CBT center mafi kusa ko kuma wadda akafi so a basu wannan profile code a inda za’ayi wannan registration.

5.        Yadda za’a dawo da profile password: za’ayi amfani da lambar da aka sayi ePin sai a rubuta “password” sai a bada space sai rubuta “email address” a tura zuwa 66015 ko 55015 ta hanyar text message

Hukumar ta JAMB ta bayyana cewar ta kara subjects guda biyu wato computer studies da Physical and Health studies. Hakan ya sanya subjects na UTME suka koma subjects 25.

YADDA ZA’A DAWO DA ePIN IDAN BAIZOBA KO KUMA IDAN YA BATA

Ga masu JAMB: Za’a rubuta UTMEPIN da lambar da akayi NIN  a tura zuwa 55019 ko 66019 a inda za’aga an turo da wannan ePin da aka rasa.

Ga masu DE: Za’a rubuta DEPIN da lambar da akayi NIN  a tura zuwa 55019 ko 66019 a inda za’aga an turo da wannan ePin da aka rasa.

Note: a tabbatar da lambar da akayi rijistar NIN aka aika wannan sako! Hukumar Jamb ta fito da sabbin USSD CODE (55019, 66019)domin saukakawa dalibai tura profile code.

Za’a fara UTME/DE Registration a ranar 12th Febuary zuwa 19th March 2022. Sai Mock registration a ranar 12th Febuary 2022 sai Mock UTME a ranar April 16th 2022. Za’a fara  Jarrabawar UTME  a ranar 6th zuwa 16th May 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button