Education

Hukumar Jamb Ta Fitar Lokacin Yin UTME/DE Da Abubuwan Da Ake Bukata

Hukumar shirya jarrabawar JAMB (Joint Admission and Matriculation Board) ta fitar da lokacin fara rijistar UTME (Unified Tertiary Matriculation Examination) da kuma DE (Direct Entry).

Za’a fara rijistar a ranar Alhamis, 8th April zuwa Asabar 15th may 2021. Hukumar ta tabbatar da ranar Asabar 5th zuwa Asabar 19th June 2021 za’a fara a kuma kammala rijistar ta UTME. Hukumar ta kara da cewar bazata kara lokaci kan lokacin da data fitar na yin wannan registration ba.

KARANTA: Bayero University, Kano Ta Saki Sakamakon Jarrabawar Post UTME 2020/2021

Wajibine Seda Nin Number Za’ayi Rijistar UTME/DE 2021

A zaman masu ruwa da tsaki na hukumar a ranar 22nd March 2021, hukumar ta tabbatar da cewar wajibine kowane dalibi sai yazamo yana da NIN (National Identification Number) kafin ayimasa rijistar UTME da DE ta shekarar 2021.

Za’ayi rijistar Jamb da DE a santoci guda 700 na duka kasa (Based Test Centers Nationwide)

Wannan sanarwa ta fito daga bakin shugaban yada labarai na hukumar Dr. Fabian Benjamin a ranar Larabar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button