Education

Hukumar NECO Ta Sanya Ranar Rufe 2021 2021 SSCE – External Registration

Hukumar shirya jarrabawar NECO (National Examination Council) ta sanar da ranar da zata rufe registration na 2021 External  SSCE (Senior Secondary Certificate Examination) ta wannan shekarar.

Hukumar ta tsayarda ranar 31st October 2021 a matsayin ranar da zata rufe wannan registration.

Shi wannan registration wanda akafi kiransa da private Neco mafiyawancin daliban da suka fadi jarrabawar Neco internal ne ke yinsa idan sun duba sakamakon jarrabawarsu baiyi kyau ba. Izuwa wannan lokaci dai hukumar bata saki wancan sakamako ba ballantana dalibai su tabbatar da kodai sun sami result na shiga jami’a ko basu samu ba ta yadda zasu yin wannan registration.

Hukumar ta sanar da wannan rufewa ne a website dinta a inda take umartar dalibai da masu kasuwancin internet café dasu hanzar kammala wannan registration kafin ranar da hukumar ta sanya.

Hukumar ta bada lambobin waya da na email ga wadanda keda wata tambaya ko korafi kamar haka:

Email: support@neco.gov.ng

Phone: 09070447255, 09026080796, 09070447254

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button