Education

JAMB TA SANARDA RANAR FARA UTME

Hukumar shirya Jarrabawar JAMB (Joint Admission and Matriculation Board) na sanarda dalibai cewar zata fara rijistar jarrabawar UTME ta shekarar 2021 a ranar 8th April 2021 a inda za’a kammala rijistar a 15th May 2021.

Hukumar ta jaddada cewar dole ne kowane dalibi yazamo yana da NIN (National Identification Number) kafin yasamu damar yin wannan rijista ta JAMB da DE, dan haka duk wanda yakeson yin JAMB KO DE ya hanzarta zuwa center mafi kusa domin yin NIN rijista.

Domin yin JAMB ko DE Rejistration sai a ziyarci Accredited CBT center ko kuma Internet Café wanda aka yadda da ingancinsa domin yin wadannan rijistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button