Education

JAMB UPDATE: AN FARA CIRE JAMB SLIP 2022

Hukumar JAMB ta sanar da fara cire result na jarrabawar UTME wadda aka kammala ta shekarar 2022

Kamar yadda kowa ya sani cewar da zarar an kammala jarrawar JAMB dalibai kan saurari lokacin da hukumar ta JAMB zata sanar das akin sakamakon ta yadda kowane dalibi kan garzaya internet café mafi kusa domin dubawa yaga abinda ya samu.

Wannan shekara lamarin ya canza daga yadda aka sani ta yadda dalibi zaije café mafi kusa ya bada JAMB Slip dinsa a dauki Registration Number ko kuma Phone Number domin dubawa.

Wannan shekarar hukumar ta JAMB ta bawa dalibai damar tura sakone kawai ta hanyar SMS a inda dalibi zaiyi amfani da layin da yayi rijistar UTME dashin ya tura sakon “UTMERESULT” izuwa 55019 a inda za’a turo masa da sakamakon nasa take.

A wannan shekarar idan dalibi nason yayi print out na result dinsa to sai ya biya kudi kamar yadda zai cire JAMB origina result ne. Hakan na iya zama wata barazana ga dubban dalibai duba da wannan kudi da hukumar ta garkama wanda zai iya kawa N2000 zuwa sama.

Duba da matsanancin tattalin arziki da ake fama dashi hakan kan iya shafar karatun dalibai da yawa a wannan shekara.

Ga dukan dalibin da yake bukatar ya fitar da sakamakon jarrabawarsa ta JAMB/UTME sai ya garzaya internet café ko JAMB CBT center mafi kusa domin biyan wannan kudi da hukumar ta kakaba domin ganin abinda ya samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button