Education

KANO STATE TABIYA KUDIN JARRABAWAR NECO WADDA AKA RIKE

Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewar ta biya Naira miliyan 100 kudin jarrabawar Neco ta daliban jihar kano da aka rike.


Gwamnatin ta bayyana cewar a ranar Litinin ne ta biya zunzurutun kudi Naira miliyan Dari da hudu da dubu Dari Uku da Sittin da Biyu da Naira casa’in (N104, 362, 090) domin sakin jarrabawar Neco wadda hukumar shirya jarrabawar Neco ta rike.


Gwamnatin ta bayyana cewar hukumar ta tabbatar mata da biyan kudin a inda nan bada dadewa ba daliban zasu iya duba sakamakon jarrabawarsu.


Wannan sanarwa ta fito daga bakin mukaddashin yada labarai na gwamnan Abba Anwar a yau Talata 16th march 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button