Education

JIGAWA STATE GOVERNMENT TA BIYA KUDIN JARRABAWAR NECO 2021

Gwamnatin Jigawa ta biya hukumar neco Naira miliyan 317 kudin jarrabawar dalibai guda Dubu Dari Takwas (800,000) jihar wadanda suka zauna jarrabawar Neco ta wannan shekara.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Director General State Education inspectorate and Monitoring Unit malam Abdullahi Yunusa a wata tattaunawa da akayi dashi da manema labarai.

Babban Jami’in ya kara da cewar gwamnatin ta biya zunzurutun kudi har Naira miliyan dari Uku da shabakwai (N317) ga hukumar Neco domin sakarwa dalibai jarrabawarsu ya kara da cewar kowane dalibi zai iya fara duba jarrabawarsa daga ranar Alhamis ko Juma’a domin ganin sakamakon jarrabawar tasu.

Babban jami’ain ya kara da cewar gwamnati zata kafa wani kwaniti wanda zai duba wadanda suka sami sakamako mai kyau domin a basu kyauta ta musamman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button