Education

Kano Science and Technical Schools Board – Sakamakon Jarrabawar 2022

Makarantar Kano Science and Technical Board sun gudanar da jarrabawar shekarar 2022 domin daukar sabbin dalibai na Junior da kuma Senior domin cigaba da karatu, kuma akalla an sami dalibai daga sassan jihar ta kano masu tarin yawa da suka zauna wannan jarrabawa.

Saidai Iyaye dalibai suna ta tambayar ko yaushe ne sakamakon jarrabawar zai futo? Hakan yasa daya daga cikin jami’an Arewatalent ya tattauna da wani Jami’in Maknatar ta Kano Science and Technical Board domin jin ina aka kwana, inda jami’in yace:

“Sakamakon jarrabawar Kano Science and Technical Board na dab da fitowa domin suna nan suna ta shirye-shirye domin sakin sakamakon jarrabawar.

Ya kauma kara da cewa akalla nan da mako 2 ko 3 sakamakon zai zama ya nuna a shafin da makarantar ta samar na yanar gizo-gizo domin gudanar da aikin yau da kullum.

Ku sasance tare da shafin arewatalent.com a ko da yaushe domin samin sahihan labarai na makarantun gida da na waje da kuma abubuwan da suka shafi harkokin ilimi.

Zamu sanar da al’umma da zarar an saki sakamakon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button