Education

MENENE JAMB GREEN CARD?

Dayawan mutane/dalibai basusan me ake nufi da Jamb Green Card ba. Shi dai  Jamb Green Card (Change of Institution/Course) wani tsari ne da Jamb, hukumar shirya jarrabawar shiga jami’oi da sauran makarantun gaba da sakandare (universities, colleges and Higher institutions)  ta samar dan bawa dalibai damar canza makaranta daga wata zuwa wata ko kuma canza kwas (courses) a jami’ar da ka nema ta hanyar tsarin e-facility.

Shikuma tsarin e-facilitywani tsari ne da hukumar Jamb ta samar don yin rigista ta Jamb (UTME) da Direct Entry (DE) da kuma sauran registration na gyaran matsalolin da dalibai ke fuskanta a yayin registration na jamb, sune kamar haka:

1.       Print Result: Ta wannan tsari ne dalibi zai cire Original Jamb Result akan kudi N 1000 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

2.       Admission letter printing: ta wannan tsari ne dalibi zai cire Admission Letter wadda jami’a ta bashi admission akan kudi N 1000 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

3.       Correction of Data: akarkashin wannan tsari akawai abubuwa da yawa kamar haka:

a.       Change of Course/institution: A wannan tsari dalibi zai iya canza course da institution da bazai iya shiga ba a sakamakon rashin kaiwar makin a jarrabawarsa ta jamb. Haka na idan makin dalibi bai kai da ya karanta wani course a jamia’ar daya nema ba zai iya canza wadannan course zuwa wani akan kudi N2500 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

b.      Change Name: idan dalibi ya samu matsala a sunansa, zai iya gyara wannan matsala ta wannan tsari akan kudi 2500 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

c.       Change of Date of Birth: Tanan ne dalibi zai iya graya shekarar haihuwarsa daya sami matsala a yayin registration. Amma fa dalibi zai cike wani form (indemnity form)wanda  za’a iya cireshi(download) a shafin Jamb sannan ya cike ya kai makarantarsa domin su tabbatar da shi (approval). Dalibi zai biya N 2500 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

d.       Change of Gender:kamar change of DOB, shima za’a cike indemnity form a mayar dashi makarantar da mutum ya nema, bayan antabbatar dashi ne zai yi printing na slip dinsa.

Change of state/LGA: dalibi zai iya canza state ko LGA dinsa ta wannan hanyar. Anan ma dalibi zai cike indemnity form kafin wannan canji yayi akan kudi N 2500 (jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

4.       Condonoment of Illegal Admission (without Registration number): wannan tsari nada fuska biyu kamar haka:-

a.       Late Application akan kudi N 3500 da kuma Condonoment of Illegitimate Admission akan kudi N 5000

Duka wadannan se ancike indemnity form a kuma yi approval, sannan za’a bawa dalibi  damar printing  registration Number.

5.       Condonoment of Illegal Admission (with Registration number): Dawannan tarsi ne dalibi zai iya cire  ainahin admission letter da yayi applying bayan daya cire sai yaga ba abinda ya nema aka bashi ba. Dalibi zai biya  N5000 sannan wajibine yazamo ya rike registration Number dinsa.

6.       Application for Change of Admission letter: Bayan da dalibi yayi printing na Admission letter se yaga ba abinda ya nema aka bashi ba to sai yabi wannan tsari don canja masa abinda ya nema akan kudi N5000. jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

7.       Retrieval of Registration Number: Idan dalibi ya manta jamb registration number dinsa zai biya don ya dawo da ita akan kudi N1000 jamb official price) amma idan kaje café zaka sami Karin kudi kadan

8.        Inter University Transfer (within Nigeria): wannan tsari na bawa dalibi damar transfer daga wata Jami’a (University) zuwa Wata a cikin Nigeria akan kudi N5000

9.       Inter University Transfer ( from foreign Universities): wannan tsari na bawa dalibi damar transfer daga jami’ar kasar waje zuwa jami’ar gida akan kudi N5000

10.   Checking Admission Status: wannan tsari na bawa dalibi damar ganin ko ya sami admission ko bai samu. Wannan tsari kyauta ne.

Don samun cikakken Karin bayani gameda jamb e-facility da dukkan programs da hukumar ke shiryawa danna wannan link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button