News

Nasarori Guda 30 Da Abba Gida-Gida Ya Cimma A Kwana 30

An haife shi a Jihar Kano, Abba ɗan Muhammadu Kabir dan Ɗanmakwayon Kano Yusuf dan Muhammad Bashir dan Galadiman Kano Yusuf ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, ɗan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ɗan ƙabilar Sulluɓawa ne na ƙabilar Genawa ta Fulani, a ɓangaren uwa kuma yana da alaƙa da Walin Zazzau Sheikh Umarul Wali ɗan Galadiman Zazzau Malam Ahmadu, kakarsa Zainab diyar Malam Saidu Limamin Huggalawa daga gidan Limamin Huggalawa ne a garin Bichi, kakarsa Khadijat Naja’atu tana da alaƙa da Gwani Mukhtar wanda shi ne jagoran Jihadin Fulani a Kanem- Daular Borno.

Yayi karatun Primary a Makarantar Sumaila Primary School, ya kammala a Shekara ta 1969-1975. sannan Yayi karatun Sakandire a makarantar Lautai Secondary School Gumel GCE 0/level- a shekara ta 1975-1980 bayan nan ya halarci Federal Polytechnic Yola Jihar Adamawa inda ya sami National diploma ta ƙasa a ɓangaren kimiya da fasaha a fanin injiniya wato(Engineering) a shekara ta 1982-1985, a Kaduna Polytechnic, yayi HND a fannin injiniya a shekara ta 1987-1989 sai kuma ya halarci Jami’ar BUK Kano, PGDM a shekara ta 1994-1995. har wayau ya samu shaidar Masters a ɓangaren karatun harkokin kasuwanci (MBA) a shekara ta 1997-1999 a Bayero University Kano BUK(Ihayatu (talk) 22:51, 30 Mayu 2023 (UTC))

Ya riƙe muƙamin Kwamishinan aiyuka a zamanin mulkin tsohon gwamnan jahar kano Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso, daga shekara ta 2011 Zuwa shekara ta 2015 sannan yayi takarar gwamnan kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a shekara ta 2019. Sannan Kuma ya sake yin takarar Gwamna a jam’iyyar NNPP a jihar Kano a shekara ta 2023. Abba yayi nasarar zama Gwamnan jihar Kano a zaɓen gwamnan Kano na shekara ta 2023 inda yayi nasara a kan babban abokin hamayyar sa na Jam’iyyar APC  Nasiru Yusuf Gawuna. An rantsar da Abba kabir yusif a matsayin gomnan jihar kano a ranar Litinin ashirin da tara 29 ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Nasarori 30 Da Abba Gida-Gida Ya Cimma A Kwana 30

Nasarori 30 a cikin kwana 30 na Maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Daga ranar 29/05/2023 da aka rantsar da mai girma gwamnan Kano zuwa ranar 29/06/2023, ya yi nasarar cimma nasarori kamar haka:

1. Janye haraji ga kanana yankasuwa masu karamin jari;

2. Daina zaftare gudin yanfansho tare kuma da yi musu kari akan ahunda su ke karba duk wata;

3. Daina zaftare N370 daga albashin ma’aikata daa ake yi babu gaira babu dalili;

4. Aiwatar da ingantaccen tsari ga alhazan Kano domin gudanar da aikin hajjin bana cikin limana;

5. Kafa kwamitin kartakwana domin tsaftace Kano;

6. Kwashe bola daga lunguna da titinan Kano;

7. Kafa kwamitin kartakwana domin yaki da masu kwacen waya da sauran miyagun laifuka;

8. Dakile matsalar kwacen waya da kuma yadda yake jawo asarar rayuka;

9. Dawo da cibiyar horar da kangararru dake garin Kiru wacce gwamnatin baya ta rufe;

10. Dawo da kunna fitilun kantiti da daddare a titinan Kano;

11. Dawo da aiki da fitilin danja (trafic light) a danjojin Kano;

12. Dawo da asibitin Hasiya Bayero da gwamnatin Ganduje ta cefanar;

13. Fara gyaran asibitin Hasiya Bayero domin ingantashi;

14. Dawo da sansanin alhazai da aka wawure a gwamnatin baya;

15. Dawo da wani sashe na filin sukuwa da aka zaftare aka baiwa danlele a gwamnatin baya;

16. Dawo da ginin Daula hotel ga jami’ar KUST domin habbaka ilimin jami’a a jahar Kano;

17. Bude wasu makarantun kwana kamar su jambaki da aka rufesu a gwamnatin baya;

18. Fara gyaran asibitin Bela domin ingantashi,

19. Kafa majalisar zartarwa tare umartar kwamishinoni da su dukufa da aiki ka’in da na’in;

20. Dawo da martabar masallacin idi da aka cefanar a gwamnatin baya;

21. Rabawa daliban sekandire mata tallafin Naira dubu ashirin ashirin a kananan hukumomi 19 a karkashin tsarin nan na Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE);

22. Biyawa dalibai kusan budu 60 kudin NECO;

23. Fara tantance dalibai da za a tura kasashen waje domin karo karatu;

24. Ayyana dokar ta baci domin tabbatar da samar da zaftateccen ruwan sha a jahar Kano;

25. Kyautata mu’amulla tare da girmama malaman jahar Kano ba tare da nuna banbanci ba;

26. Inganta mu’amulla da yankasuwa tare da neman shawararsu akan wasu muhimman abubuwa. Misali, gwamna ya nemi shawararsu akan ya yakamata ayi da gineginen babban layi da aka yi a kasuwar wambai, da kuma wadanda aka yi a kasuwar kantin kwari;

27. Inganta kyakkyawar alaka da bangaren majalisa;

28. Inganta kyakyawar alaka da ciyamomin kananan hukumomi ba tare da nuna banbancin jam’iya ba;

29. Dawo da gidan gwamnatin Kano da ke Kwankwasiya city da gwamnatin baya ta cefanar;

30. Dawo da anfani da bus bus da ke daukar dalibai mata domin kaisu makarantunsu.

Za a iya samun wasu nasarorin bayan wadannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button