Education

NIGERIAN COLLEGE OF AVIATION TECHNOLOGY ZARIA ADMISSION 2021

Ina wadanda basu sami admission na shiga cillage ba kuma suna da burin karatun Engineering musamman wanda ya shafi tuki ko gyaran jirgi to ga dama ta samu. Hukumar makarantar Nigerian College of Aviation technology zaria ta fara bada admission na shekarar 2021

Hukumar makarantar na sanarda duk wanda keda maki 120 zuwa sama na Jamb daya garzaya zuwa website na  makarantar domin cikewa ko kuma wadanda suke da bukatar canzawa zuwa wannan makaranta dasu ziyarci Jamb portal domin su canza a official website na Jamb https://www.jamb.gov.ng/caps ko kuma a CBT center mafi kusa  domin canzawa.

Nigerian College of Aviation na gabatar da wadannan courses kamar haka:

  1. ND Electrical Engineering/Electronics Engineering
  2. ND in Aircraft Maintenance Engineering

Abubuwan da ake bukata domin shiga wannan makaranta:

  1. O level Result wanda ya hadar da English Langauge, mathematics, Physics, Chemistry da kuma kowanne sauran subject
  2. Jamb point 120 zuwa sama wanda ya hada mathematics, Physics da Chemistry

Domin cike wannan makaranta sai a ziyarci www.ncat.gov.ng domin cikewa a kuma dora O level result bayannan sai a a duba cikin email a inda za’aga sako idan makarantar ta bada admission. Wadanda basu saka wannan makaranata a first choice ba baza su sami admission ba har sai sun maida wannan makaranta a first choice a Jamb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button