Recruitment

Yadda akeyin Rijistar Sabon Tallafin Covid-19 Support

Sabon tsarin tallafin Korona na wannan karon yazo ne ta sabon portal wanda Nirsal Micro Finance Bank suka sake domin Kara tsaro da kuma inganta tsarin.

Saidai mutane da yawa suna fuskantar kalubale wajen cike sabon tsarin da kansu, hakan ne yasa arewatalent team sukayi Karin haske ga al’ummar kasarnan wadanda suke da sha’awar cikewa suna daga gida.

Yadda ake cikewa:

Dafarko za’a shiga cikin sabon Portal Nirsal Micro Finance Bank link: Apply Now

Bayan ka shiga akwai tsari na tallafin rancen har kala uku amma wanda yake abude a yanzu shine Non Interest TCF da kuma Non Interest AGSMEIS.

Cikin wadan nan zaka iya zabar guda daya daga cikinsu ko dai House hold ko kuma SME Facility.

Yadda Ake Cike na Households:

Dafarko za’a fara validating na BVN domin a tabbatar babu wani bashi akanka, bayan an tabbatar daganan sai a dora rijistar.

Abinda ke hana rijstar tafiya bayan an gama:

Bayan gama cike komai daga bayanai zuwa sauran duk abinda ake bukata, sai a kula akwai wajen cike kudin abubuwan da kake bukata a kauwancin naka, wannan waje ka tabbata kudin da ka sanya kada ya wuce  naira dubu dari biyar 500,000  domin idan ya wuce haka rijstar baza ta tafi ba har sai an saita sannan sai ya wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button