Education

Yadda Zaka Samu 9 Credits A Jarrabawar Waec Ko Neco 2020/2021

Barka da zuwa shafin Arewa Talent a wannan lokaci Insha Allahu zamu fada muku hanyoyin da zakubi ku sami 9 Credits a Waec da Neco.

Read more: Yadda Ake Dawo da National ID Card Idan Yabata ko An Sace 

Samun a kalla 5 credits wanda ya hadar da Math da English jarrabawar WAEC ko NECO  kan bawa dalibi dammar shiga jami’a, polytechnics ko colleges. Ta haka ne mukai duba kan wata sahihiyar hanya wadda idan dalibi bawai kadai 9 credits kawai zai samu ba har ma da yiwa kyakkyawar shinfidar zama nagartaccen dalibi a duka inda ya samu dammar yin karatu. Ga duk daliban da ke fannin karatun kimiyya da fasaha da ma wadanda ke bangaren karatun koyan kasuwanci da dai sauransu, zasu biyo wannan tartibiyar hanya don cimma burinsu na zama abinda suke son zama ta bin wannan hanya. Jarrabawar Waec ko Neco akan shirya ta ne cikin jadawalin jarrabawar shekara biyar, wato ana shirya jarrabawar da za’ayi alal misali jarrabawar shekara ta 2020 daga 2014 zuwa 2019. Ta haka ake tsamo tambayoyin da za’a shirya wannan jarrabawa.

Wannan hanya itace kamar haka:

Step 1: Zaka samo jarrabawar da akayi (past questions) ta shekara biyar a koawanne subjects (e.g English, Mathematics, Economics Government etc).

Step 2: Zaka iya faraway da English alal misali, sai ka dauko tambayara farko ta English ta shekara ta 2014 har izuwa ta shekara ta 2019, sai ka amsa su a lokaci daya.

Step 3: Sai ka tafi izuwa tambaya ta biyu a English kayi kamar yadda kayi a tambaya ta daya. Haka zakayi har izuwa karshen tambayoyin.

Step 4: Bayan ka gama amsa English, sai ka tafi izuwa Mathematics kayi mata kamar yadda kayi ta English. Duka sauran subjects din ma haka zaka yi musu.

Kafin ka gama wannan bita a kanka zakaga cewar lallai ka gamsu cewar zaka iya samun 9 credits a kodai Waec ko Neco, domin zakai ta karo da makamanta ko ma sak irin tambayar da ka amsa a cikin wata jarrabawar da ka amsa.

Rubutu Masu Alaka

Read more: Al-Qalam University, Katsina Cut-Off Mark 2020/2021

Read more: Kokasan Tayaya Zaka Samu Kudi da InksNation? 

Read more: Yadda Zaka Duba Date of Birth Dinka Dakasa a BVN Dinka 2020  

Read more: Bashi Wanda Babu Ruwa Kwatata Acikinsa 2020

Domin neman karin bayani ko kuma bamu wata shawara akan wani abu zaka iya ajiye mana comment a kasa ko kuma ka tuntubemu ta wadannan hanyoyi kamar haka.

Email: aminubyusuf20@gmail.com

WhatsApp: +2348054173837

Facebook: Arewa Talent

Instagram: ArewaTalent.Com.Ng

 YouTube Channel: Al’ameen Tech

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button