Technology

BANKIN ZENITH YA KADDAMAR DA SABON JADAWALIN BUDE ACCOUNT TA WhatApp (Intelligent Virtual Assistance)


Bankin Zenith a kokarinsa na bunkasa harkokinsa na kasuwanci da kwastomominsa ya yunkura ya fito da wani jadawalin mai suna Intelligent Virtual Assistance (ZiVA) wanda zai bawa dukkan masu ma’amala dashi damar cigaba da mu’amala kai tasye dashi ta hanyar kafar sadarwar WhatApp

Wannan sabuwar hanya na amfani da manhajar WhatApp a inda bankin ya samar da wannan lamba 07040004422 domin ganawa da jami’an bankin ta kafar sadarwar whatApp.

Bankin ya jera wadannan abubuwa domin more hurda da bankin a sawwake kamar haka:

•             Bude  zenith bank Account

•             Dawo da zenith account number data dade ba’a amfani da ita (domant)

•             Tura kudi izuwa kowane account a Nigeria

•             Dai daita hada hadar account dinka

•             Shiga da duba matsalar makalewar kudi (dispense error)

•             Duba account balance

•             Siyan data da airtime

•             Rufe katinka (ATM)

•             Neman bashi

•             Da sauransu da dama

Bankin na kara kira da kwastominsa dasu rungumi wannan sabuwar fasaha don inganta ma’amalarsu da bankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button