Technology

Whatsapp Application Yasamu Kishiya

An kaddamar da sabon application mai suna Signal, wannan application yana dauke da abubuwa masu ban sha’awa, kuma wannan application na Signal suna kamanceceniya da application na WhatsApp, Amma sai dai kishiya ne na WhatsApp sakamakon wasu tsare-tsare dayazo dasu na idan ka tura sako na rubutu ko na murya ko kuma na hotuna zaka iya saitawa sakonnin su ringa bacewa duk mako ko kuma duk wata.

Abubuwan da Application na Signal yakunsa:

Ana kirkirar Group kamar yadda ake kirkirar Group na WhatsApp, saidai shi wannan application hada jama’ar Group dinsa yasha banban da na WhatsApp, domin shi ba za’a iya daukar lambar wani ba don sanya shi acikin group har sai ya amince.

Shima ana iya tura komai na sakonni kama daga Murya, Rubutu, GIF, da kuma files.

Wannan application na Signal ana yin Video Call dashi da kuma kira na murya a duk inda mutum yake a fadin duniya, kuma batun sauti yana fitar da murya tangaran kamar gaka ga wanda ka kira, a game da Video fitowa ne kawai mutum ba zai yi ba, ma’ana tar-tar zakaga komai.

Domin samun wannan application saika danna wannan link: Signal Private Messenger

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button