Technology

Yadda Zaka Duba Plastic National ID Card Dinka 2021

Wannan application yana dauke da abubuwa da dama daga ciki zai nuna maka yadda Date of Birth dinka yake da kuma yadda Sunanka yake a jere, sannan kuma yazone a nau’in Plastic mai gaba da baya, wanda idan kataba gaban katin zai juyomaka da bayansa.

Shekarun baya mutane dayawa sunyi National ID Card amma sun manta yaya Date of Birth dinsu yake ko kuma da wacce lambar waya sukayi a yayin rijistar, tunda in anyi duba da Slip din da ake printing baya nuna wadannan abubuwan da aka ambata a sama.

Rubutu Masu Alaka:

Yadda Ake Amfani da Mobile App Na National ID Card | NIMC MWS Mobile ID App

Cikakken Bayanin Yadda Ake Gyara Date of Birth Na National ID Card

Amma a yanzu wannan matsala takau domin wannan sabon application na national id card ya kunshi dukkan bayanan da ake bukata.

Kadan Daga Cikin Damar da Wannan MWS: NIMC Mobile ID Kedashi:

Sannan akan samu wadanda lambar wayarsu ta bata to ta hanyar wannan app za’a iya ganin wani bangare na lambar wayar, a inda hakan zai sa a tuna lambar da akayi amfani da ita.

Bugu da kari bayan NIMC Mobile ID App din ya hau kan wayarka zaka iya duba bayanan ka dare ko rana ba tare da amfani da Data ba.

Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da wannan NIMC Mobile ID App ya kunsa, wanda anan gaba akwai abubuwa da dama da za’a dinga yi dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button