Technology

Cikakken Bayanin Yadda Ake Gyara Date of Birth Na National ID Card

Matsalar gyara shekaru a jikin National Id Card abu ne da yazama ruwan dare dalili kuwa shine, Arewa Talent na karbar wasiku na al’ummar wannan kasa daga lungu da sako akan wannan matsala.

Hakane yasan ya kwararrun ma’aikatan mu sukayi bunciken tsaf akan yanda za’a warware wannan matsala da kuma magantata.

READ MORE: MTN Capture Customer NIN Details

Tabbas wannan matsala ta gyara Date of Birth na National Id Card ta dade a damfare da mutane amma basu sani ba, sai da aka zo yin abubuwa kamar su BVN da kuma abubuwan da suka shafi harkar bude Asusu (Bank Account) daga nan irin wannan matsaloli suka fara tasowa.

Hanyoyin Gyarawa Sune Kamar Haka:

Kafin mutum yaje a gyara masa Date of Birth na National Id Card akwai kudi da ake biya ta Remita.

Yadda Ake Biyan Kudin:

Abu na farko za’a ziyarci shafin remita.net. Bayan mutum ya shiga daga sama zai ga ansa Search Here for a biller saika rubuta National Identity Management Commission.

Daga nan zai bude maka wani shafi a shafin zakaga ansa (Name of Service/Purpose) saika danna shi kana dannawa saika zabi wannan (Correction Of Date Of Birth (Day, Month, Year Or All).

Bayanka danna daga nan zai bude maka form wanda yake dauke da:

  • Kudin da zaka biya (N15,000.00)
  • Sunan wanda zai biya (Payer’s name)
  • Lambar waya ta mai biya (Payer Phone)
  • Sai adireshin Email (Payer Email)
  • Saika kara sanya email dinka a akwatu na gaba (Confirm Email)
  • Akwai akwatu mai rarrabe tsakanin mutum da butun butumi (I’m not a robot) saika danna wannan alama.
  • Daga nan sai alamar kore mai dauke da rubutu (Submit) saika danna wannan alama.

Daga nan kuma bayanka danna wannan submit zai sabekane izuwa fejin dazaka biya kudin a wajen biyan kudin akwai hanyoyi guda (8) amma hanyoyi uku sunfi saukin biya.

  • Card
  • Bank Branch
  • USSD

Hanyar biya da Card (Debit Card/ATM Card), shine zaka cike gurabe da aka bayar a shafin kuma bayanan da zaka sanya suna jikin katin bankin naka, bayan kagama za’a cire kudin daga Account dinka, sai ayi download na shaidar biya.

Hanyar biya ta Bank Branch shine zakai Printing na Invoice saika tafi da ita izuwa banki mafi kusa da kai saika biya daga nan banki zasu baka shaidar biya.

Hanyar biya ta USSD shine zaka zabi bankika daga nan zakaga an kawo maka lambobin da zakayi amfani dasu domin biyan kudin, bayan ka biya zai baka shaidar biyan kudin saikayi printing dinta.

Akarshe dukkan hanyar da kabi daga cikin ukun da muka kawo muku mafi sauki wajibine kayi printing na shaidar biyan kudi domin da ita wannan shaidar biyan kudinne za’a tafi ofishin National Identity Management Commission mafi kusa da kai, ma’aikatansu zasu karba daga nan sai ayi wannan gyara na Date of Birth.

Idan ba za’a iya kudin ba ta wadannan hanyoyi da muka kawo ba za’a iya ziyartar Internet Café mafi kusa domin biyan kudin.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button