Technology

Yadda Ake Amfani da Mobile App Na National ID Card | NIMC MWS Mobile ID App

A ranar 31 December, 2020 Hukumar NIMC ta saki sabon Mobile ID App ga al’ummar Najeriya gaba daya.

Duba da yadda bukatar National ID Card yataso ga tsofaffi da matasa musamman yadda National Id Card din a yanzu dolane sai an hada shi tare da abubuwa da dama kamar su layikan waya (SIM Card), International Passport da kuma abubuwan da suka shafi bude Asusun ajiya (Bank Account).

Wannan ya sanya hukumar NIMC yin wannan application mai matukar mahimmanci, domin sauwakewa al’ummar kasa wajen ganin bayanan da National ID Card dinka ke kunshe dashi ko kuma yin Printing dinsa a lokacin da akeso.

Kuma wannan application yana da cikakken tsaro sannan an hade shi da hukumomi kamar su Driver’s License, Health Card, Tax Clearance (FIRS), Departure Card, Nafdac, Voter’s Card da sauransu.

Yadda Ake Shiga NIMC MWS Mobile ID App da Abubuwan da Ake Bukata:

  • Abu na farko shine ana bukatar National Identification Number (NIN) ma’ana wadannan nambobi goma sha daya na jikin National ID Card dinka.
  • Abu na biyu shine Lambar wayarka: Anan ana nufin lambar wayar da kayi amfani da ita a lokacin da kayi National ID Card domin ta wannan lamba ne za’a turo da wasu Lambobi wadanda ake kira a turance (OTP), Saboda dasune za’a gane kaine domin baka damar karasa dora app din akan wayarka.  
  • Abu na uku shine: a lokacin da zaka dora wannan app a wayarka ana bukatar cikakken service (Internet Connection), saboda idan yakasance babu service mai kyau a lokacin da ake dora wannan application to ba zaiyi daidai ba ko kuma yaki baka damama gaba daya.

Yadda Ake Download NIMC MWS Mobile ID App

Get in touch with us:

Facebook: Arewa Talent

WhatsApp: +2347067399944

Telegram: ArewaTalent.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button