Technology

Hukumar NCC Tayi Mobile App Domin Sauwaka Rijistar Katin Dan Kasa (NIN)

Ministan sadarwa da fasahar zamani Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, FNCS, FBCS, FIIM, ya amince da ci gaba da kuma fitar da ingantaccen takardar shaidar dan kasa (NIN) da kuma mobile App.

Wannan yana daga cikin Manufofin Gwamnatin Tarayya domin inganta aikin samar da NIN da kuma hadashi shi da layukan waya (SIM cards)  wanda aka aika zuwa Hukumar NIMC (national Identity Management Commission) da kuma Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC(National Communication Commision) domin gabatarwa. Domin saukakawa, gwamnati ta cire N20 da N40 ake cajar mutane don tantancewa.

 

Gwamnatin ta samar da wannan shiri dan karfafa  kudirin da ta gabar na hada NIN da SIM card wanda aka tattabatar a farkon wannan shekara 4th February 2020.

Gwamnatin ta samar da sassaukar hanyar yin NIN wanda keda cikakken tsaro da  aka kirawo shi NINC Mobile App  wanda a yanzu kowa zai iya samunsa. Hakanan kuma shi wannan mobile App zai bawa duka “yan kasa kariya da kuma mahukunta(legal residents) domin tabbatar da bayanai a nan take ta hanyar amfani da wayar hannu. Sannan kuma zai bawa mutum damar hada NIN dinsa da wayarsa ta hannu.

Wannan sabon tsari zai taimakawa gwamnati wajan hade dukkan bayanan mutum a gwamnatance wanda ya hadar da NCC, Federal Inland Revenue Service, federal Road safety commission  da National Health Insurance Scheme da sauransu domin sawwaka ayyukanta. Shi wannan sabon NIMC mobile App nada saukin amfani a inda mutum kan iya duba NIN dinsa ta wayarsa ya kuma sauke shi da sauran dukkan bayanansa. Za’a cigaba da amfani da NiN slip wanda mutane ke dashi a yanzu a inda za’a cireashi nan a hankali.

Za’a iya samun wannan sabon App ga masu wayar Android a Google Play store sai kuma masu iOs a App store. Cikakken bayanin yadda za’a cire wannan App na nan a shafin NIN da kuma social media na hukumar. Mutane zasu iya downloading wannan App a https://dashboard.ninc.gov.ng

Me girma ministan ya umarci hukumar NIMC  dasu tabbatar sun amsa dukkan wata tambaya da mutane suka nema sannan da su wayarwa wa mutane kai gameda wannan sabon tsari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button