Education

How to apply into Aminu Dabo College of Nursing Sciences

Yadda za’a cike makarantar koyon kiwan lafiya ta Aminu Dabo College of Nursing Sciences kano

Domin cike wannan makaranta sai a bi wadanan matakai kamar haka:

Bayan an shigo website na makarantar https://adcons.edu.ng

Mataki na farko shine  Account Activation:

1. Za’a danna New Application

2. A shigar da Suma, valid phone number(ka tabbatar lambar wayar tana aiki)

3. Fejin zai kaika inda zaka shiga wato LOGIN

mataki na Biyu:

Zakayi amfani da lambar wayarka da shigar a farko wadda itace zata zama Username da Password naka. Sai ka danna kashiga cikin fejin

Mataki na uku:

Zakaje gurin biyan kudi. Ka tabbatar ka sanya sunanka dai dai sannan ka biya kudin, bayan biyan kudin sai ka cike dukkanin bayananka.

Mataki na hudu:

Za’a zabi programme da ake son yi daga jerin courses da makarantar ke gabatarwa.

Mataki na biyar:

Za’a sanya educational qualification wato takardun makaranta kamar WAEC/NECO da dai sauransu. Ba’a bukatar sama da zama biyu na jarrabawa. A tabbatar an sanya kara kara inda aka zauna jarrabawa sannan a sanya exam number ta fito sosai.

Mataki na shida:

Za’a dora photo. A tabbatar an sanya photo wanda zaa iya gane mutum sannan yazamo yanada fari ko wata kala wadda zaa iya gane mutum. Hoton yaza a JPEG yake sannan kada nauyinsa ya wuce 150kb.

Mataki na bakwai:

Bayan antabbatar an cike bayanai dai dai, sai a tura wannan apllication.

Mataki na takwai:

Za’ayi printing na Application form. Zaaga lambar waya wadda aka cike ita zata Application ID sannan kuma itace Login details. Sai ayi printing na Application form.

Mataki na tara:

Kafin a Nada admission sai an tabbatar da wadannan abubuwa kamar:

I. Wajibi a halarci screening, ba wakilci ba

2

II. Wajibi azo gurin screening da  dukkan takardun makaranta da wadanda aka cire a yayin application

Iii. Za’a bada photocopy na wadannan takardu

iv. Za’a bada photocopy na indigene letter da takardar haihuwa

Matakai na goma:

Makarantar zatayi amfani da lambar wayarka wajan tuntuba gameda lokacin da zaa gudanarda wannan screening.

Domin karin bayani gameda wannan makaranta sai a tuntubi wadannan lambobin waya na makarantar 07942800003, 07042800004, 08042800005

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button