Technology

YADDA ZAKA SABUNTA KATIN ZABENKA – INEC

Hukumar zabe ta kasa wato INEC (Independent National Electoral Commission) ta shirya domin baiwa “yan kasa wadanda basuyi register ta katin zabe (Voter Card) ba da wadanda suke da gyara ko canza inda zasu karbi katin zabensu damar yin wadannan abubuwa a sawwake a shafinta na yanar gizo.

Hukumar ta dora muhimman alamura daban daban musamman abinda ta samar me lakabin ” Continuous Voter Registration Portal) a inda kowanne dan kasa zai iya shiga ya duba bukatarsa ya cike ya tura online.

Ga jerin abubuwan (Services) da hukumar ta samar kamar haka:

  1. New Voter Registration: hukumar ta samar da wannan tsari domin wadanda basuyi register ba su sami damar yi kamar wadanda shekarunsu yakai 18
  2. Voter information Review: Domin duba yadda bayananka suke akan katin zabenka
  3. Locate Registration Centers: Domin sanin inda santocin yin zabe suke akoina a fadin kasa ta yadda zaka iya zuwa mafi kusa dakai ka kammala register
  4. Transfer: idan kana son canza inda zaka ringa yin zabe.
  5. Information Update: Domin gyara ko canza bayaninka na katin zabe
  6. Uncollected PVC: Domin karbar katin zabenka
  7. Lost or Damaged PVC: idan ka rasa ko katin zabenka ya lalace zaka iya dawo dashi
    Domin ziyartar wannan shafi na INEC sai a danna wannan official INEC link:

Za’a iya aikwa hukumar saka kai tsaye ta email ko ta waya a:
icc@inec.gov.ng
070022554632

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button