Education

Zaka Iya Gyara Subject Na Jamb 2022 A Kowace CBT Center Kyauta

Hukumar JAMB ta bayyana yadda za’a gyara subjects na UTME ga wadanda suka sami matsala a yayin registration na wannan shekarar.

An sanyawa dayawan dalibai subjects da basu suka zaba ba a yayin cike form na JMAB/UTME hakan yasa hukumar shirya jarrabawar ta bawa daliban da suka fuskanci wannan matsala damar gyarawa.

Hukumar ta bayyana cewar dalibi zaije kowane CBT center dake a fadin kasar nan  domin gyara matsalar subject wadda ya fuskanta.

Hukumar ta bayyana cewar wannan gyara kyauta ne ba’a bukatar bada ko dari domin wannan gyara. Don haka ake bukatar da a sanar da wadanda suka fuskanci irin wannan matsalar domin magancewa.

Lokacin da aka bada domin wannan gyara takai tacce ne, ya kamata duk wanda yasan yanada wannan matsala daya hanzarta zuwa CBT center mafi kusa da shi domin ganin ya maganta wannan matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button